Wuta ta kone mutane biyu tare da motoci 30 a Lagos


Mutane biyu ne suka mutu motoci 30 kuma suka kone a wata wuta da ta kama da safiyar yau a Ijegun dake jihar Lagos.

Gobarar ta tashi ne sakamakon ayyukan wasu barayin man fetur.

Wutar ta kama da misalin karfe 5 na asuba bayan da wasu mutane dake satar mai suka kammala dibar mai daga wani bututu da suka fasa a yankin.

Mazauna yankin sun rika gudun tsira da rai sa’ilin da bututun ya fashe inda wutar ta rika yaduwa a yankin.

Jaridar The Cable ta gano cewa mutanen da ake zargi da satar man suna sanye ne da kayan sojoji da kuma na yan sanda domin gudun kada su samu turjiya daga mutanen yankin sa’ilin da suke aikata ta’asar.

A cewar hukumar bada agajin gaggawa ta jihar Lagos barayin sun gama cika tankar mai guda daya da man fetur mai cin lita 33,000 inda suna kan cika ta biyu ne jami’an tsaro suka farmusu.

A lokacin da suke kokarin tserewa jami’an wani man fetur din ya kwarara cikin magudanar ruwa inda ake zargin barayin kunna masa hana jami’an tsaro bin su.


Like it? Share with your friends!

-1
74 shares, -1 points

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like