Wata sabuwa: Faruk Lawan ne ya keta sakamakon zaben gwamnan Kano – Inji Sulen Garo


Kwamishinan harkokin kananan hukumomi na jahar Kano, Alhaji Murtala Sulen Garo ya musanta zargin da ake masa na sa hannu cikin tayar da hankali a ofishin hukumar INEC ta karamar hukumar Nassarawa tare da mataimaki gwamna Nasiru Yusuf Gawuna da har ta kai ga sun yaga sakamakon zaben gwamna na karamar hukumar.

Majiyarmu ta Sahara Reporters ta ruwaito Murtala ya bayyana haka ne a ranar Alhamis, 14 ga watan Maris a yayin ganawa da yayi da yan jaridu a ofishinsa, inda ya ambaci sunan tsofaffin yan majalisar wakilai, Farouk Lawan da Nasiru Sule Garo a matsayin wadanda suka kekketa sakamakon zabe na mazabar Gama.

Idan za’a tuna, hotunan kwamishina Murtala da mataimakin gwamna Gawuna sun bazu a shafukan sadarwar zamani, yayin da wasu matasa suka kama shi babu ko riga a jikinsa, daga bisani Yansanda suka kwace shi, har sai da ya kwana a hannunsu.

Sai dai a jawabinsa, Garo ya zargi jam’iyyar PDP da shirya wannan labarin kanzon kurege, inda yace magoya bayan PDP ne suka rirrike shi da nufin hana shi shiga ofishin hukumar INEC, a dalilin haka ne suka kekketa masa riga.

Ya kara da cewa shi da Gawuna sun isa ofishin ne a lokacin da suka samu labarin Farouk Lawan da Nasiru sun isa ofishin yayin da tattara alkalumman sakamakon zabe da nufin tayar da hankali, har ma suka kekketa sakamakon zaben ba tare da wani yace musu uffan ba, hatta Yansanda basu yi musu komai ba.

Daga karshe Murtala yace “Bamu da cikakken yakini game da kwamishinan Yansandan jahar Kano, saboda yana goyon bayan ta’adin da PDP ke shiryawa a jahar Kano, baya mana adalci.” inji shi


Like it? Share with your friends!

-1
101 shares, -1 points

Comments 2

Your email address will not be published.

You may also like