Wata matar aure mai suna,Bilkisu Abubakar ta fadi ta mutu jim kaɗan bayan da suka gabza fada da kishiyarta, Hajara Abubakar.

Dukkansu na auren miji daya ne a kauyen Jiramo dake karamar hukumar Takai ta jihar Kano.

Mai magana da yawun rundunar yansandan jihar Kano, DSP Abdullahi Kiyawa wanda ya tabbatarwa da jaridar Daily Trust faruwar lamarin, ya ce lamarin yafaru ne ranar Laraba da misalin karfe goma na dare.

Ya ce dagacin garin Fajewa, Alhaji Yau Hamza shine ya kaiwa yansanda rahoton faruwar lamarin.

Ya ce dagacin yaje ofishin ƴansanda tare da Hajara matar da ake zargi.

A cewarsa matar da ake zargi ” sun samu sabani da marigayiya kishiyarta har ta kai ga sunyi fada a sakamakon fadan ne Bilkisu ta yanke jiki ta fadi ta mutu nan take,” ya ce tuni aka kai gawar marigayiyar asibiti.