wata mai yin madarar Peak ta jabu ta fada hannun jami’an tsaro


Hukumar dake kare hakin masu amfani da kayayyaki ta sake samun karin nasarar kwace madarar Peak ta jabu a kasuwar Eziukwu dake garin Aba a jihar Abia.

Ya yin samamen da jami’an hukumar suka kai sun samu nasarar kama wata mata dake samar da madarar ta jabu kana ta bayar da bayanai kan wasu mutane da suke taimaka mata wajen rabawa da kuma sayar da madarar.

Tuni jami’an hukumar ta CPC suka mika ta hannun jami’an tsaro domi cigaba da bincike da kuma gurfanar da matar gaban shari’a.

A kwanakin baya ma sai da aka samu nasarar kama wasu dake aikata irin wannan algus a kasuwar Wuse dake Abuja.


Like it? Share with your friends!

2

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like