Wata kungiya ta maka hukumar yan sanda da EFCC a kotu, tace lallai sai an binciki Ganduje


Wata kungiyar jama’a mai suna Enough is Enough (EiE) Nigeria, ta maka hukumar yaki da cin hanci da rashawa a gaban wata babbar kotun tarayya da ke Abuja akan zargin cin hanci da ake yiwa Abdullahi Ganduje, gwamnan jihar Kano.

Kungiyar ta ambaci sunayen hukumar yaki da rashawa ta ICPC da rundunar yan sanda a cikin wadanda ake kara a cikin takardar karar.

A watan Oktobar shekarar da ta gabata ne jaridar Daily Nigerian ta wallafa wasu bidiyo daban-daban da ke nuna Ganduje yana karban rashawa daga hannun yan kwangila, amma gwamnan ya karyata zargin.

Hakazalika majalisar dokokin Kano ta kafa kwamitin mutum bakwai domin bincike akan lamarin gwamnan, sai dai babbar kotun jihar ta dakatar da majalisa daga binciken.
Amma kungiyar ta EiE caccaki martanin hukumomin akan lamarin.

A wani jawabi da ta saki a ranar Talata, 14 a watan Mayu, Tolulope Oladele, mataimakiyar manajan kungiyar, tace kungiyar ta jajirce domin neman jawabi daga zababbun jami’an gwamnati a kasar.

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like