Rundunar yan’sandan jihar Nassarawa a ranar Litinin tace jami’anta biyu yan bindiga suka kashe akan hanyar Akwanga zuwa Keffi.

Kennedy Idrisu, mai magana da yawun rundunar yan’sandan jihar ya tabbatarwa da kamfanin dillancin labarai na ƙasa NAN faruwar lamarin.

Yace rundunar ta tura jami’anta daga ɓangaren dake yaƙi da fashi da makami da yan sandan kwantar da tarzoma da kuma yan kungiyar bijilante domin su bincike dajin dake wurin inda ake zargin wata matartara ce ta masu aikata kisan kai.

Ya ce wurin da lamarin yafaru an gano cewa wata cibiya ce da masu garkuwa da mutane da kuma aikata sauran manyan laifuka me cin karensu babu babbaka.Shine dalilin da yasa rundunar ta girke jami’anta a wurin.

Mai magana da yawun rundunar yace mummunan abin da yafaru bazai saka gwiwarsu tayi sanyi ba wajen kare da dukiya da kuma rayukan al’umma.