Wasu masu garkuwa da mutane akan hanyar Kaduna-Abuja sun fada hannun jami’an tsaro


A cigaba da kokarin da take na raba hanyar Kaduna zuwa Abuja da masu garkuwa da mutane da kuma yan fashi da makami, rundunar yansandan Najeriya ta samu nasarar kama wasu masu garkuwa da mutane da kuma barayin shanu.

An samu nasarar kama mutanen ne ranar 11 ga watan Mayu dauke da bindigogi biyu kirar Ak-47, gidan harsashi guda biyar, harsashi 54, bindigogi kirar gida guda 5 da kuma shanun sata 200.

Mutanen da aka kama sun hada da Ayuba lawal, Saidu Bello, Abdullahi Bello, Adamu Lawal, and Umar Sani dukkaninsu yan asalin karamar hukumar Dan Musa ta jihar Katsina.

Jami’an sun samu nasarar kama su ne a Dajin kudaru dake karamar hukumar Lere ta jihar Kaduna bayan kwararan bayanan sirri da rundunar ta samu daga wasu mazauna yankin.

Sauran wadanda aka kama da zargin yin garkuwa da mutanen sun hada da Muhammad Sani, Jibrin Shehu, Usman Sani, Musa Garba jami’an tsaro sun kama sune a Dajin Akilbu dake karamar hukumar Kachia.

Dukkanin mutanen da aka kama sun bada bayanai gamsassu kan rawar da suka taka wajen yin garkuwa da mutane da dama akan hanyar Abuja zuwa Kaduna.


Like it? Share with your friends!

1
101 shares, 1 point

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like