Wasu Inyamamurai Biyar Sun Amshi Addinin Musulunci


Ga abinda Malama Aishat Obi ‘yar kabilar Ibo dake da’awar jawo ‘yan uwanta Inyamurai cikin addinin musulunci ta rubuta a shafi ta na facebook:

“Allahu Akbar, Asalamu alaikum ‘yan uwana musulmai maza da mata. Ku taya ni murnar shigowar wasu ‘yan yankunan kudu maso kudu da kudu maso gabashin kasar nan cikin addinin musulunci a jiya a garin Fatakwal.

Sunayen su sune kamar haka:

(1) Believe Isaiah (Sehid Isaiah) (daga jihar Rivers)

(2) Okechukwu Onwusaraka (Isan Onwusaraka) (daga jihar Imo)

(3) Chinonso Onyejiako (Hassan Onyejiako) (daga jihar Imo)

(4) Ngozi Uwa (Nafisa Hassan) (daga jihar Imo)

(5) Oluchi Eze (Khadija Eze) (daga jihar Imo)

Malama Aishat Obi ta kuma yi fatan Allah ya kare ta tare da ba ta nasara a da’awar da take yi don ganin ta jawo ‘yan uwanta Inyamurai cikin addinin Musulunci.


Like it? Share with your friends!

7
70 shares, 7 points

Comments 2

Your email address will not be published.

You may also like