Wasu Ingantattun Hanyoyi da Buhari Ya Kirkiro Don Hana Jami’an Gwamnati Satar Kudi


Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya samar da wasu hanyoyi ko dabaru guda goma da ya kirkiro domin amfani dasu wajen yaki da rashawa a gwamnatinsa, tare da hana jami’an gwamnatinsa satar kudaden al’umma, kamar yadda jaridar Premium Times ta rawaito.

Buhari ya fidda sabbin dokokin ne bayan wani bincike da yasa wasu kwararru suka yi ne a kamfanoni da hukumomin gwamnati guda goma sha biyar da suka binciko an gano wasu kudi naira Triliyan 8.1 da basu shigar asusun gwamnati ba a tsakanin shekarar 2010 zuwa 2015.

Da wannan dalilin ne Buhari ya kirkiri dokoki guda goma da zasu tabbatar da dukkanin kamfanoni da hukumomin gwamnati da suke tattara kudaden haraji suna shigar da duk kudaden da suka samo ga lalitan gwamnati, ba tare da ko kwandala ta yi ciwon kai ba.

Daga cikin kamfanonin da wadannan sabbin dokoki zasu shafa akwai hukumar kula da tashoshin jiragen ruwa NPA, hukumar kula da hanyoyin ruwan Najeriya NIMASA, hukumar tattara kudaden haraji, FIRS, hukumar kula da jiragen kasa NRC, hukumar kula da iskar gas NGC, JAMB, NNPC, NTA, NDIC, NCC da sauransu.

Sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha ne ya sanar da haka cikin wata takardar aiki da aka rarraba ma hukumomin a ranar 16 ga watan Oktoba wanda tace an yi haka ne don tabbatar da kamfanonin da hukumomin sun daina cutar da gwamnati.

Daga cikin dokokin guda goma sun hada da;-

1- Za’a sanya iyaka ga shuwagabannin hukumomin

2 – Babban Akanta na kasa zai dinga lura da ayyukan hukumomin tare da bayyana rahoton wata wata

3 – Za’a dinga duba ayyukan dake cikin kasafin kudinsu duk bayan wata uku

4 – Za’a rage yawan tarukan hukumar gudanarwa, tafiye tafiyen kasashen waje da almubazzaranci

5 – An tilasta ma hukumomin su dinga amfani da asusun bai daya na TSA

6 – Gwamnati zata dinga amsan kudaden da suka tattara duk bayan watanni uku uku

7 – Za’a kara kaimi wajen bin diddigin harkokin kudaden hukumomin

8 – An iyakance adadin kudin da za’a dinga basu ga ayyukan da suka zama wajibi akansu

8 – Tilas su dinga mika kasafin kudinsu ga ofishin kasafin gwamnati

9 – Babban akanta na kasa ne zai aika da kwararren jami’in da zai kula da sashin kudi na hukumomin


Like it? Share with your friends!

3
104 shares, 3 points

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like