Wasu gwamnonin jihohin Arewa 3 na kan hanyar komawa jam’iyar PDP


Wasu gwamnonin jihohin Arewa su 3 da aka zaba karkashin tutar jam’iyyar APC suna kan hanyarsu ta komawa jam’iyar PDP kowane lokaci daga yanzu.

Sanatoci masu yawa da yawansu ya kai 30 da kuma yan majalisar wakilai 70 ana sa ran za su bi bayansu kafin majalisar kasa ta fara hutu nan da makonni biyu masu zuwa.

Masu shirin sauya shekar sun fito ne daga jam’iyar rAPC bangare jam’iyar APC da ya balle.

Yawancinsu sun kasance ƴaƴan jam’iyar PDP kafin su fice daga cikin ta a shekarar 2013.

Aminu Waziri Tambuwal, gwamnan jihar Sokoto, Abdulfatah Ahmad gwamnan jihar Kwara da kuma Samuel Ortom gwamnan jihar Benue na daga cikin rukunin farko da ake sa ran za su fice daga jam’iyyar.

“Tsarin shine wasu daga cikin gwamnonin APC baza su sauya sheka ba za su cigaba da zama domin yiwa jam’iyar babbar illa,” acewar wani gwamna da ya fito daga kudancin kasarnan a hirar da ya yi da Jaridar The Cable.


Like it? Share with your friends!

-3
98 shares, -3 points

Comments 1

Your email address will not be published.

You may also like