Wasu gwamnonin APC sun bukaci a cire shugaban jam’iyar Adams Oshimhole


Wasu gwamnonin jam’iyar APC na bukatar a cire shugaban jam’iyar na kasa, Adams Oshimhole daga kan mukaminsa.

Wani minista da ya nemi a boye sunansa shine ya sanar da manema labarai haka ranar Laraba.

Adawa da salon mulkin Oshimhole na zuwa ne kasa da watanni hudu cikin wa’adin mulkinsa.Ya karbi jagorancin jam’iyar daga hannun John Oyegun cikin watan Yuni wannan shekara.

Ministan ya ce fusatattun gwamnonin sun ki amincewa su bayar da gudunmawar kudi ya yin babban taron jam’iyar inda suka ce a jam’iyar ya yi amfani da kudin da ya tara daga sayar da fom din takara.

“Wasu daga cikin gwamnonin da basu ji dadin salon mulkin Oshimhole ba sun fadawa shugaban kasa Muhammad Buhari cewa dole ne Oshimhole ya kauce idan har ana so jam’iyar ta yi nasara a babban zaben shekarar 2019,”ya ce.

“Sun dage cewa dole Oshimhole sai ya tafi saboda ba za su iya aiki da shi ba a zaben shekarar 2019. Sun ki bayar da gudunmawar kudin a babban taron jam’iyyar inda suka nemi shugaban jam’iyar ya yi amfani da biliyan goma da ya tara na sayar da fom din takara.Suna kuma bibiyar yadda ya kashe kudaden.’

Ministan ya ce tabbas an tattauna batun sauke shugaban a ganawar da gwamnonin suka yi da shugaban kasa.

Gwamnan jihar Zamfara, Abdulaziz Yari ya fito fili ya soki shugaban jam’iyar wanda ya bayyana da cewa ya nuna iko sai kace wan karamin allah.

Comments 2

Your email address will not be published.

You may also like