Wasu batagari sun kona ofishin hukumar zabe a Akwa Ibom


Wasu batagari sun kona ofishin hukumar zabe ta kasa INEC dake karamar hukumar Ibesikpo Asuntan a jihar Akwa Ibom.

Kayayyakin zabe sun kone kurmus a gobarar da ta faru ana gab da zaben gwamnoni da na yan majalisun dokokin jihohi daza a gudanar ranar Asabar.

Jihar Akwa Ibom na daga cikin jihohin da aka samu yawan tashin hankula a zaben shugaban kasa da kuma na yan majalisun tarayya.

Rikicin siyasa yayi kamari a jihar ta Akwa Ibom mai arzikin man fetur dake yankin kudu maso kudu,tun bayan da tsohon gwamnan jihar,Godswill Akpabio ya sauya sheka daga jam’iyar PDP mai mulkin jihar ya zuwa jam’iyar APC.

Wasu hotuna da kuma fefan bidiyo da suka karade kafar sadarwar zamani sun nuna yadda yansandan squka kama yan bangar siyasa masu yawa dake kan hanyarsu ta zuwa jihar daga jihar Edo.

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like