Wani Yaro dan shekara 13 ya mutu a cikin ruwa a Kano


Wani yaro dan shekara 13 mai suna Dayyabu Salisu ya nutse a ruwa lokacin da yake wanka a wani kududdufi dake kauyen Yankatsari a karamar hukumar Dawakin Kudu dake Kano.

Mai magana da yawun hukumar kashe gobara ta jihar Kano ya fadawa kamfanin Dillancin Labaran Najeriya NAN cewa lamarin yafaru ne a ranar Laraba da safe lokacin da marigayin yaje wanka.

Muhammad ya ce” mun samu kiran kai daukin gaggawa daga wani mutum mai suna Mallam Aminu Sani da misalin karfe 10:25 na safe inda ya ce anga gangar jikin Salisu na yawo akan ruwa kududdufi.

“Muna samun kiran mun tura jami’an mu dake aikin ceto zuwa wurin da misalin karfe 10:55.

“Mun samu Salisu a mace kuma daga bisani an mikawa mahaifinsa,Mallam Salisu Abdullahi gawarsa,” ya ce.


Like it? Share with your friends!

1
72 shares, 1 point

Comments 2

Your email address will not be published.

You may also like