Wani Wanzami Ya Babbake Kansa Har Lahira


Ya mutu a wani asibiti yayin da yake amsar magani bayan mutane sun kai masa ɗauki.

Majiyarmu ta jaridar PUNCH ta kawo rahoton cewar an ga mai askin ranar laraba da misalin karfe huɗu da rabi na yamma rike da jarkar fetir lita biyar.

Ba a farga ba sai kawai aka ga ya soma bulbula fetir ɗin a jikinsa, sannan daga bisani ya kyasta wa kansa ashana.

Majiyar tamu ta kara da cewa wani mutum da ke tsaye can gefensa ne yai ta maza ya tunkare shi domin ya kashe masa wutar.

An ce matashin mai askin wanda aka bayyana sunanshi a matsayin Ahmad, ya riga mu gidan gaskiya ‘yan lokuta kaɗan bayan ‘yan kwana-kwanan Jihar Legas sun tserar da shi.

wani mutum mai suna Dolapo Gabriel da ke gurin da abin ya faru ya gaya wa jaridar PUNCH cewar, “Kafin bayyanar jami’an kwana-kwana da ‘yan sanda gurin, wani mutum ya ɗauki yagaggen kwali inda ya dinga yin fiffita ga mai askin. Sai dai a lokacin da yake kokarin tserar da rayuwar Ahmad ɗin, wasu tarin mutane a can gefe ba abin da suke sai ɗaukar hotunansa da wayoyinsu.

Gabriel ya kara da faɗin cewa a da Ahmad ɗin yana da shagon da yake yin aski kafin ya canja ya ɗauki wani salon rayuwa na daban.

“Na ganshi lokacin da yake bulbula fetir ɗin a jikinshi, amma na zata ruwa ne. A cikin ‘yan sakanni sai ya ɗauko kwalin ashana daga aljihunsa ya kyasta wa kansa. Cikin sa’a wata mai sayar da abinci a kusa da gurin tana da ruwa. A gaggauce wani mutum ya ɗauki ruwan ya sheka masa. Ban taɓa ganin irin wannan abun ba a rayuwata.

Wani mazaunin gurin da ya bayyana sunanshi a matsayin Tolu, ya ce, ya ga Ahmad ranar Litinin yana tafiya a kan hanya sai ya bashi shawarar ya canja salon rayuwar da ya ɗaukar wa kanshi.

Ya kara da cewa, “A da Ahmad ɗin ma’aski ne, kuma yana da shago a Akiode. Daga baya sai ya rufe shagon ya koma yawace-yawacenshi a unguwa. Bayan nan sai kuma ya faɗa harkar shaye-shaye wanda ina ganin shi ya taɓa masa kwakwalwa.

“Kwanaki biyu da suka wuce na haɗu da shi a kan titi har nai masa magana kan yana bukatar canjin hali. Na ce masa zan kai shi coci ranar Lahadi domin a yi masa addu’a ta musamman. Daga nan ya roke ni da in saya masa gasasshiyar masara. Na yarda na saya masa masarar bayan ya tabbatar min cewar zai bi ni cocin.”

Wani ganau ba jiyau ba, Samuel, ya bayyana Ahmad a matsayin ɗan kwaya. Ya kara da faɗin cewa Ahmad ɗin ya ɗan jima da zarewa sakamakon shaye-shayen.

Samuel ya kara da faɗin “Mutane da yawa da ke nan gurin sun san shi. A da mutumin kirki ne kafin daga baya ya koma shan kwaya. Yana zaune da danginsa a wannan gurin, kuma suna sane da halayyar da ya sanya kansa.

Wani babban jami’in ‘yan kwana-kwanan ya gaya wa majiyarmu cewar Ahmad ɗin ya mutu yayin da yake amsar kulawa a Asibiti.

“Cikin rashin sa’a bamu iya ceton rayuwarsa ba. Ya mutu a lokacin da yake amsar kulawa, sannan mun damka gawarsa ga danginsa.”

Kakakin rundunar ‘yan sandan Jihar Legas, CSP Chike Oti, ya tabbatar da faruwar abun, amma ya ce har yanzu bai samu cikakken bayanin mutuwar mutumin ba.

Kakakin ya ce, “Abun ya farua gaske. Mutumin ya yi yunkurin kashe kansa ta hanyar kona kansa, amma an cece shi. Har yanzu bamu samu takamaiman dalilin da ya sa ya aikata irin wannan mummunan aikin ba.


Like it? Share with your friends!

-1
76 shares, -1 points

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like