Wani Soja Ya Harbe Kansa Da Matarsa Bayan Ya Gano Cewar ‘Ya’ yansa Guda Biyu Na Wani Ogansa Ne


Wani soja ya harbe matarsa har lahira bayan ya gano cewar wasu yara guda biyu da ya rika ba nasa bane, sannan mahaifinsu na ainahi wani soja ne da ke gaba da shi a aiki. Lamarin ya faru a wata barikin soji inda matar tasa ta kulla wata alaka da ogansa.

Majiyarmu ta samu rahoton cewar wani sojan kasar Zambiya mai suna Pathias Mwape ya samu jita-jitar ‘ya’yansa guda biyu da yake rike da su ba nasa bane, sannan da ya tunkari matar tasa wacce ‘yar sanda ce, sai kawai ta fashe da kuka tare da tabbatar masa cewar gaskiyane yaran ba nasa bane.

Wani soja ya ce, “Jita-jita ta yi ta kewaya na wasu lokuta. Abin da mu dai muka sani shine matar tana kwanciya da wani oganmu. An yi imanin yaran nan guda biyu na Ogan ne, amma shi mijin matar shi ne ya raine su har zuwa yau. Ya shiga dimuwa sosai da safe. Bayan ya harbe matar sai ya fita neman ogan. Ya so ya harbe shi shima, amma sai akai dace ogan da iyalinsa basa nan.”

“Shekarun baya lokacin da ya tafi aikin wanzar da zaman lafiya, wani daga cikin oganninmu ya dinga zuwa gidansa yana kwanciya da matarsa. Labari ne sananne. Manyan oganninmu sun sani sannan muna saurare mu ga ko in za a yi hukunci dai-dai da tsarin dokarmu.”

Wani jami’i a barikin Kabwe Chindwin ya bayyana cewa manya-manyan sojoji a bariki suna jin dadin kwanciya da matan sojojin da ke kasa da su. Mwape ya yi amfani da karamar bindiga gurin harbe matarsa jiya. Lokacin da ya gane ‘yan sanda na nemansa ruwa a jallo sai shima ya harbe kansa.

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like