Wani shugaban karamar hukuma ya sha duka a jihar Jigawa


Wasu magidanta da suka fusata sun lakadawa, Bala Yargaba , shugaban karamar hukumar Dutse dukan tsiya.

Mazauna yankin sun zargi yar gaba da kin biyan kuɗin akwati wani kuɗi da gwamnati ke bawa duk wata cibiyar zaɓe domin gudanar da ayyukan ci gaban jama’a. Inda suka bukaci biyan kuɗin.

Ya yin da yake kokarin yiwa taron jama’ar da suka taru bayani kan yadda ake raba kuɗin ka wai sai suka farmasa.

Suka riƙa yi masa ihu suna fada masa bakaken maganganu ya yin da wasu suka keta masa babbar riga.

Bayan da taron jama’ar suka ci zarafinsa daga baya ya samu nasara shiga cikin sakatariyar karamar hukumar.

Fusatattun mutanen sun yi wa sakatariyar kawanya inda suka hana shi futa daga ciki.

Da aka tuntube shi kan lamarin Yarbaga ya yi zargin, cewa Musa Sule, wakili a majalisar dokokin jihar shine ya turo mutanen domin su muzanta shi.

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like