Wani mutum ya yanke jiki ya fadi matacce a wata tashar mota dake jihar Lagos


An gano gawar wani mutum mai matsakaicin shekaru wanda aka rawaito ya fadi ya mutu a tashar motar Orinle-Iganmu dake jihar Lagos.

Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya, NAN ya rawaito cewa mutumin yazo wucewa ne inda yanke jiki ya fadi da safiyar ranar Talata.

Yinus Olayiwola wani mai sayar da kaya a wurin da lamarin yafaru yace anga marigayin yana rawar ɗari a wurin da misalin ƙarfe 6:30 na safe.

Yanayin rashin lafiyar mutumin ya ta’azzara ne sakamakon dan yayyafin ruwa da aka rika yi da safiyar.

Wani mazaunin yankin mai suna Bamidele Adejoke ya bayyana rashin jin dadinsa kan yadda gawar marigayin ta dauki tsawon sama da awanni 8 kafin hukumomin da abin ya shafa su zo su dauke ta.


Like it? Share with your friends!

-1
103 shares, -1 points

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like