Wani matashi ya yiwa yarinya ‘yar shekara uku fyade


Wata kotun majistire dake Kano ta bayar da umarnin tsare wani mutum mai suna, Khalid Abdullahi a gidan yari kan zargin yin lalata da wata yarinya yar shekara uku.

Abdullahi dake zaune a unguwar Yankaba dake Kano na fuskantar tuhumar aikata fyade da ya saba da sashi 283 na kundin Penal Code.

Alkalin kotun, Muhammad Jibril ya bayar da umarnin a tsare wanda ake zargi a gidan yari kana ya dage shari’ar ya zuwa ranar 28 ga watan Oktoba.

Tun da farko dan sanda mai gabatar da kara,Insifecta Pogu Lale ya fadawa kotun cewa wani mai suna, Muhammad Saddam mazaunin unguwar Badawa shine ya shigar da korafin faruwar lamarin a ofishin yan sanda na Bompai dake Kano ranar 22 ga watan Satumba.

Ranar 21 ga watan Satumba da misalin karfe biyu na rana mutumin da ake zargi ya yaudari tare da hilatar yarinyar cikin gidan yayarsa dake saman bene inda ya aikata lalata da ita.

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like