Wani Matashi Ya Yiwa Ecobank Kutse Ya Saci Naira Miliyan 207


An gurfanar da wani matashi dan shekaru 28 a gaban kuliya a sakamakon tuhumar shi da ake yi da yin kutse a manhajar bankin Eco inda ya saci Naira miliyan 207.

Matshin mai suna James Nwagalezi ya aikata wannan laifi ne tare da wani mai suna Okoli Nmesoma, wanda tuni aka fara yi masa shari’a.

Dan sanda mai kara, Insfekta Jimoh Joseph ya fadawa kotun cewa matashin tare da wasu da yanzu haka ake neman su sun aikata laifin ne a ranar 27 ga watan Afrilu a yankin Okokomaiko da ke Ojo a jahar Lagos.

Ya ce bankin ne ya kai karar faruwar lamarin ga DPO na ofishin ‘yan sandan Ikoyi, Tijjani Mustapha, inda daga nan ne aka shiga neman su.

Bayan da aka shafe watanni ana nema ne aka kama Nwagalezi, wanda shi ne na 6 a jerin wadanda aka kama game da laifin.

Lafiin ya saba da sashe na 411, 387, 287 da 325 na kundin dokar jahar Lagos.

Sai dai Nwagalezi bai amsa laifin ba.

An bada belin shi akan Naira miliyan daya, tare da bukatar masu tsaya masa guda biyu.

An daga sauraren karar zuwa ranar 4 ga watan Yuli.


Like it? Share with your friends!

2
123 shares, 2 points

Comments 4

Your email address will not be published.

You may also like