Wani matashi ya nutse cikin ruwa a Kano


Wani matashi mai shekaru 22 ya nutse a ruwa lokacin da yake tsaka da wanka a wani kududdufi dake garin Danhassan a karamar hukumar Kura ta jihar Kano.

Mai magana da yawun hukumar kashe gobara ta jihar Kano, Mallam Sa’idu Muhammad shi ne yana bayyana haka cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi.

Ya ce “Mun samu kiran kai daukin gaggawa daga wani mai suna, Mallam Sadi Ibrahim da misalin karfe 03:31 na rana inda ya ce anga gangar jikin Abdullahi na yawo akan ruwa.

“Da samun kiran, mun tura jami’an mu na aikin ceto inda suka isa wurin da misalin karfe 03:42.

“An ciro gawarsa inda aka mika ta ga, Alhaji Aminu dagacin kauyen Garin Kaya.”

Ya ce ana cigaba da bincike domin gano musabbabin mutuwarsa.


Like it? Share with your friends!

0

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like