Wani makiyayi ya kashe ɗansanda a jihar Kebbi


Wani makiyayi mai suna, Babuga Kaura ya kashe wani ɗansanda, Umar Danladi a garin Kaoje na karamar hukumar Bungudo dake jihar Kebbi.

Rundunar ƴansandan jihar Kebbi ita ta tabbatar da faruwar haka ranar Alhamis.

Marigayin na aiki ne da caji ofis din ƴansanda na Ka’oje dake karamar hukumar Bungudo ta jihar.

Wani manomi ne ya kai karar Kuaara bayan da ya yi zargin cewa shanunsa sun lalata masa amfanin gona.

Wani da ya sheda abinda ya faru kuma ya nemi a boye sunansa ya fadawa yan jaridu cewa an nemi marigayin da ya kama makiyayin wanda ke cigaba da kiwo da shanunsa a yankin.

“Ɗansandan wanda ya zo da bindigarsa ya kama mutumin da ake zargi amma yayin da yake tafiya da shi ya zuwa cikin motar sinitiri ta yan sandan ka wai sai makiyayin ya ciro adda kuma ya sare shi a wuya,” shedar ya ce.

Mai magana da yawun rundunar ƴansandan jihar Kebbi, Mustapha Suleiman ya fadawa manema labarai cewa tuni a aka kama mutumin da ake zargi.


Like it? Share with your friends!

-2
66 shares, -2 points

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like