Wani Magidanci Ya Yi Mutuwar Ƙarya Dan Kawai Ya Daina Aikowa Matarsa Kudi


Wannan mutum mai suna Danny Gonzalez, mai shekaru 27 mazaunin kasar Amurka ne. Amma yana da mata wacce take zaune a garin Saba dake kudancin kasar Honduras.

Gonzalez ya sa an ɗauke shi a hoto a kan gado hancinsa da baki toshe da auduga. ya kuma rufe jikinsa da farin yadi. Wato hoton yana nuna a mutuware yake. Sannan kuma ya tura wani hoton na jana’izar wata gawa duka ya aike su ga matarsa. Inda ya nuna mata sakon daga wani yake ana sanar da ita rasuwar mijinta wanda ya mutu sakamakon cutar daji (kansa) da kuma Asma.

Daga jin labarin, matarsa ta yi maza ta je kafafen yaɗa labarai ta sanar. Daga nan suka shiga aikinsu. Har dai labarin ya iske iyayensa tsofaffi da danginsa da suke a kauye. Kafin wani lokaci, sai aka gano ashe duk bula ce. Domin waɗanɗa suka yi wa hoton kurilla sun gani cewa, a kan gado aka ɗauka ba a mutuware ba. Sannan kuma rigar fulo ya rufa a jikinsa a matsayin ƙlikaffani. Wannan karya ta Gonzalez ta yi wa iyayensa ciwo har suka yi Allah wadai da shi.

Shi kuma a nasa ɓangaren, Gonzalez ya bayyana wa ‘yan jaridu cewa ya shirya wannan abu ne saboda matarsa ta saurara masa da kawo-kawo. A cewarsa matarsa ba ta taɓa yi masa waya ko aikawa da sako don ta gaishe shi ba sai domin ta nemi kuɗi a wajensa. Ga ta da rashin godiyar Allah. Duk satin Duniya sai ta nemi ya yi nata aiken kuɗi. Banda wayoyin salula waɗanda ya turo mata sun kai guda shidda amma sai ta ce wai an sace su. Shi kuma kawai sai ya shirya hakan don ya samu ya sarara.

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like