Wani magidanci da aka bayyana da suna Eyom ya mutu lokacin da yake tsaka da yin lalata da wata matar aure a wani otal dake karamar hukumar Yakur ta jihar Cross River.

Rahoton da jaridar Vanguard ta rubuta ya bayyana cewa matar auren mai suna, Grace Edin Okori sun je wurin biki ne tare da maigidanta amma ta nemi izninsa cewa za ta je wani wuri ta dawo ashe otal ta nufa wurin farkanta.

Suna tsaka da yin jima’i ne dai Eyom ya fara zubar da kunfa ta bakinsa kafin daga bisani ya ce ga garinku nan.

Bayan da ya mutu ne matar ta sulale ta gudu daga otal din inda ta koma wajen bikin kafin daga bisani ma’aikatan otal din su gano abin da ya faru inda suka je wurin da jami’an tsaro aka tafi da ita.

Tun da farko abokanan marigayin sun fada cewa ya sheda musu a ranar zai sadu da wata farkarsa kuma yana so ya burge ta sosai saboda haka yana bukatar maganin karfin maza.Wani