Wani likitan bogi ya fada komar ya sanda


Rafiu Ibrahim likitan bogi dake gudanar da wani haramtaccen asibiti ya fada hannun jami’an yan sanda dake aiki a sashen binciken manyan laifuka na rundunar yansanda shiya ta 11 dake Osogbo.

Mutumin da ake zargi wanda ke da shedar takardar kammala sakandare ya shafe lokacin mai tsawo yana gudanar da asibitin a wani gidan kasa mai daki daya inda yake duba marasa lafiya dake da cutuka daban-daban.

Bayanan sirri sun nuna cewa likitan bogin ya dade yana kwantar da marasa lafiya tare da zubar da ciki da kuma maganin cututtuka da suke da wuyar sha’ani inda yin hakan ke jefa rayuwar mutane cikin hatsari.

Mutumin da ake zargin ya amince da aikata laifin amma ya dora alhakin haka kan rashin aikin yi.

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like