Wani kason na yan majalisar wakilai za su fice daga jam’iyar APC


Abdulrazak Atunwa, guda cikin yan majalisar wakilai 37 da suka sauya sheka daga jam’iyar APC ya ce akwai karin wasu yan majalisar da za su fice daga jam’iyar.

Atunwa wanda ya koma jam’iyar PDP ya ce sauya shekar tasu kason farko ne cikin jerin mambobin majalisar da za su fice daga jam’iyar.

Ya ce jama’a su sa ran cewa mambobi da dama sun nuna sha’awarsu ta fita daga jam’iyyar.

Atunwa ya ce APC jam’iya ce da dukkaninsu sukai aikin ginata lokacin da mutane suka fito daga sauran jam’iyu daban-daban su kai yakin neman zabe suka kuma kafa gwamnati.

Dan majalisar ya ce abin takaici bayan da aka rantsar da gwamnati a watan Mayun shekarar 2015 jam’iyar ta kauce daga kan turbar da aka kafata.

Atunwa ya kara da cewa masu sauya shekar suna son cigaba tattalin arzikin kasa da kuma girmama doka da oda.


Like it? Share with your friends!

1
81 shares, 1 point

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like