Wani Jigon APC A Gombe Ya Koma PDP, Ya Caccaki Gwamnati Kan Almundahana Wajen Ciyar Da Dalibai
Wani babban jigo kuma tsohon dan kakarar gwamnan jihar Gombe a karkashin inuwar jam’iyyar APC Muhammad Barde ya sauya sheka zuwa jam’iyyar adawa ta PDP.

Muhammad Barde ya sanar da hakan ne a wajen wani taro da aka yi a jihar ta Gombe, inda kuma ya ja kunnen gwamnatin kan rashin ciyar da daliban makarantun gwamnati a jihar.

Barde yace akan ware naira miliyan 49 ga makarantun sakandare 42 a jihar, da ke da yawan dalibai 16,411 a kasafin kudin jihar a duk shekara, inda ya bayyana hakan a matsayin wata kulalliya ta yin almundahana.

Ya ce gwamnatin jihar tana amfani ne da naira miliyan 49.9 wajen ciyar da daliban a shekara guda, wanda hakan ke nufin tana kashe naira 8 a wuni, ko naira 2 da kwabo 70 ne kacal don ciyar da kowane dalibi sau uku a rana.

Da yake jawabi a wurin taron,shugaban jam’iyyar PDP a jihar Manjo janar Abnor Kwaskebe mai ritaya, yace wasu na kan hanyar komawa jam’iyyar PDP a jihar.

Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin ita kan ta jam’iyyar ta PDP mai adawa take rasa manyan jiga-jiganta, ciki har da gwamnoni, da suke sauya sheka zuwa jam’iyyar APC mai mulki a sassan kasar daban-daban.


Leave your vote

You may also like

Log In

Forgot password?

Forgot password?

Enter your account data and we will send you a link to reset your password.

Your password reset link appears to be invalid or expired.

Log in

Privacy Policy

Add to Collection

No Collections

Here you'll find all collections you've created before.