Wani ginin bene ya rufta da mutane a Ibadan


Wani ginin bene ya ruguzo a yankin Bode dake Ibadan babban birnin jihar Oyo.

Wata majiya dake yankin ta shedawa jaridar The Cable cewa lamarin yafaru ne da misalin karfe 05:50 na yamma.

Ruftawar ginin na zuwa ne kasa da sa’o’i 48 bayan ruftawar wani ginin bene dake dauke da makarantar firamare a yankin Itafaji a jihar Lagos inda akalla mutane 20 suka rasa rayukansu.

Ana tsammanin cewa mutane da dama sun makale a cikin ginin benen.

Mai magana da yawun rundunar yansandan jihar Oyo,ya tabbatarwa da kamfanin Dillancin Labaran Najeriya cewa ana cigaba da aikin ceto a wurin da lamarin yafaru.

“Abin da yafi muhimmanci a yanzu shine kawar da baraguzan ginin, domin ceto mutanen da suka makale bayannan kuma sai tantance wadanda abin ya rutsa da su,”ya ce.


Like it? Share with your friends!

-1
63 shares, -1 points

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like