Bayan ya yi nasarar yin garkuwa da wasu mutane a uku a kasar Ghana, inda ya nemi iyalansu da su biya milyoyin kudi, kuma ya ce shi dan ta’addan Bafulatani ne daga Nijeriya, sunansa Buba Muhammad.

Daga bisani dai ya shiga hannun hukumar ‘yan sandan kasar ta Ghana, inda aka gano ya kashe mutane ukun da ya yi garkuwa da su.A yayin bincike an gano cewa sunan dake jikin fasfo din sa ba shi da nasaba da Fulani (sunansa Samuel Udoetuk) daga garin Fatakwat jihar Ribas. Kuma ko kalma daya bai iya furtawa na yaren Fulatanci ba, idan ban da cewa da ya yi ya san akwai Fulani a garin Jos.