Wanda Yafi Kowa Tsayi A Duniya Ya Hadu Da Wacce Ta Fi Kowa Gajarta a Duniya


Mutumin da ya fi kowa tsayi a kundin tarihin duniya Sultan Kosen daga kasar Turkiyya, da kuma wacce ta fi kowa gajarta a duniya Jyoti Amge daga kasar Indiya an gayyace su hasumiyar Giza da ke kasar Misira ranar Juma’a.


Sultan ya samu kambun mafi tsayi na duniya a 2009 yayin da tsayin sa ya kai Santimita 243, kana kuma daga nan ya ci gaba da sambada tsayi har sai da ya kai Santimita 251 a shekarar 2011.


Jyoti Amge wacce ta samu kambun mafi gajarta ta duniya a 2011 an auna tsayin ta Santimita 62.8 ta fito a fina-finai da dama da suka hada da fim din ban tsoro na kasar Amurka ‘Body Shock’ da kuma fim din Indiya mai suna ‘Pan Suri’.


Sultan ya zama zankalele ne sakamakon wata lalurar Suburbuda tsayi da ya hadu da ita mai suna ” Pituitary Gigantism”

Jyoti Amge ta samu lalurar gajarcewa ne mai suna ‘achondroplasia’ wacce ba za ta kara tsayi daga yadda ta ke ba.


Like it? Share with your friends!

-13
109 shares, -13 points

Comments 8

Your email address will not be published.

You may also like