Wakilan kungiyar kwadago na ganawa da bangaren gwamnati


Mambobin kwamitin nan mai wakilai daga bangarori uku (Gwamnatin tarayya, gwamnatocin jihohi, ƙungiyar Kwadago) dake tattaunawa kan mafi ƙarancin albashi na nan suna tattaunawa domin lalubo mafita da ka iya kai wa a janye batun tafiya yajin aiki a gobe Talata.

Ganawar na gudana ne a ofishin sakataren gwamnatin tarayya.

Cikin wakilan dake halartar taron akwai wakilan kungiyar kwadago dana ma’aikatan masana’antu masu zaman kansu da kuma manyan jami’an gwamnati.

Ana sa ran mambobin kwamitin za su rattaba hannu a rahoton karshe kan mafi karancin albashi kana su mikawa sakataren gwamnatin tarayya, Boss Maigida Mustapha shi kuma ya mikawa shugaban kasa, Muhammad Buhari.

Ƴaƴan kungiyar kwadagon sun ci alwashin tsunduma cikin yajin aiki daga daren ranar Talata matukar gwamnati ta gaza cika musu bukatunsu.


Like it? Share with your friends!

0

You may also like