Wai Shin Haka Al’adar Hausawa Ta Koma?


A zamanin da, an san Bahaushen mutum da kunya da sanin yakamata, sannan kuma duk duniya bahaushen mutum ta tabbatar da cewa bahaushen mutum yana da rikon addini dai dai gwargwado. Har ake ganin ma a duka al’adun duniya, al’adar hausawa tana daya daga cikin al’adar da tayi dai dai da koyawar addinin musulunci.

Sai dai kash, yanzu al’adar hausawan da muka sani mai dauke da abubuwan da suke tafiya dai dai da Addinin islama babu ita. Hausawan da muka sani da kunya, yanzu babu kunyar. Hausawa sun dauki al’adun wasu mutane ko kuma ince turawa sun yafa.

Abin yana ɓata min rai idan na duba yadda Hausawa suke sahun gaba wajen aikata abubuwan da Addinin Islama ya haramta ko kuma abubuwan da Addini baizo dasu ba.

Yazo a hadisin NANA AISHA (R.A) cewa, duk wani abu wanda babu shi a cikin addini to kar muyi koyi dashi. Amma a wannan zamanin, duk abin da babushi a cikin addini, yinsa shine birgewa, in bakayi tofa kai za’ai maka kallon cewa baka waye ba. Wacce irin wayewa ce tafi wayewar addinin musulunci?

Me na gani da har yasa nake wannan rubutu?

Me mene PRE WEDDING PICTURE?

PRE WEDDING PICTURES wasu yanayin hotuna ne da hausawa suke dauka a wannan zamani na kafin aure. Ana daukar hotunan ne da salo kala kala. Salo irin wadanda ƙiri-ƙiri haramun ne. Namiji zai dauki hoto yana rungume ko yana sumbatar budurwar da bai riga ya aure ta ba. Kuma saboda rashin kunya ta wannan zamani, irin wadannan hotunan ake yaɗawa a kafafen sadarda domin nuna farin cikin za’ayi aure. Abinda basu sani ba shine, haramun ne namiji da mace suyi wata alaƙa ta taɓa juna ko sumbatar juna ba tare da aure ba. Shima irin wannan wani yanayi ne na zina wanda kuma Allah(S.W.T) ya haramta.

Mun fara zamantakewar mu akan haramun kuma muyi tunanin cewa Allah zaisa mana albarka bayan bamuyi masa biyayya ba wajen kauracewa abinda baya so.

Shiyasa yanzu aure baya dadewa zakaga ya mutu. Toh dama bamu fara ginin akan koyarwar addini ba.

Ni dai ba malami bane, amma na tabbatar da cewa wannan al’ada ta PRE wedding pictures haramun ce.

Allah yasa mu gyara.


Like it? Share with your friends!

-3
59 shares, -3 points

Comments 2

Your email address will not be published.

You may also like