Uwajumogu sanatan mazabar arewacin Imo ya mutu


Benjamin Uwajumogu, sanata mai wakiltar mazabar Imo ta arewa, ya mutu.

Wani makusancin sanatan shine ya fadawa jaridar The Cable haka, ranar Laraba.

Marigayi sanatan ya yanke jiki ya fadi inda aka dauke shi zuwa asibiti dake Abuja anan likitoci suka tabbatar da mutuwarsa.

Mutuwar sanatan ita ce mutuwar dan majalisar tarayya ta biyu da aka samu tun bayan da aka ƙaddamar da majalisar kasa ta tara cikin watan Yuni.

Ja’afar Iliyasu Auna dan majalisar wakilai daga jihar Neja ya mutu a farkon a wannan watan.

Uwajumogu na cikin koshin lafiya a jiya Talata inda har ya tofa albarkacin bakinsa kan muhuwarar da ake yi a majalisar dattawan.

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like