Unguwannin Afrika Ta Kudu Sun Ba Inyamurai Wa’adin Su Bar Musu KasaKungiyar ‘yan Nigeria mazauna kasar Afirka ta kudu (Iyamurai) sun koka yadda wasu alummomin unguwanni biyu na kasar suka basu wa’adin su gaggauta tattara komatsansu su bar musu unguwanni.

Shugaban kungiyar mai suna, Ikechukwu Anyene, yace unguwar Kuruman dake arewacin gundumar Cape sun basu wa’adin zuwa alhamis su bar musu unguwa.

Ya kara da cewa alummar unguwar Klaafontein ma, Extension 5, dake garin Johannesburg, suma sun umurci masu bada gidajen haya da kada su sake sabunta hayar wani iyamuri dan Nigeria a unguwar domin Iyamuran na bata musu tarbiyyar yara wajen sayar da miyagun kwayoyi da karuwanci.

Don haka iyamuran suke kira da gwamnatin Nigeria da ta gaggauta shiga tsakani dangane da irin karan tsanar da suke fuskanta a Afirka ta kudu.

Comments 0

Your email address will not be published.

Unguwannin Afrika Ta Kudu Sun Ba Inyamurai Wa’adin Su Bar Musu Kasa

log in

reset password

Back to
log in