Ukraine ta kama hanyar zama mamba a EU | Labarai | DWKungiyar tarayyar Turai za ta yi wani zama, don tattauna yiyuwar amsar kasashen Ukraine da Moldova a matsayin mambobi a cikin kungiyar. Ukraine na fatan ganin ta samu sahalewar EU ta la’akari da barazanar da ta ke fuskanta daga Rasha da ta kaddamar da yaki a kanta. Wannan zai kasance matakin farko daga cikin matakan da ake bukata kafin zama cikakken mamba a kungiyar.

Da yake amsa tambayoyi daga manema labarai a gabanin zaman taron, shugaban majalisar EU Charles Michel ya ce, kungiyar na fuskantar wani yanayi mai cike da sarkakiya amma hakan ba zai hanata nazari don cimma matsaya kan tsaro da daidaiton al’amura a yankin da ke fuskantar tarin kalubale musanman batun makamashi da akasarin kasashen Turai ke dogaro da Rasha a yayin da Mosko ke ci gaba da mamayar makwabciyarta Ukraine.
 
Leave your vote

You may also like

Log In

Forgot password?

Forgot password?

Enter your account data and we will send you a link to reset your password.

Your password reset link appears to be invalid or expired.

Log in

Privacy Policy

Add to Collection

No Collections

Here you'll find all collections you've created before.

omg