Najeriya ta ce kamfanin Twitter ya aiko mata da sakon neman a yi zaman sasanta takaddamar da ke faruwa a tsakaninsu.

Ministan yada labarai, Alhaji Lai Mohammed ya fadawa manema labarai a fadar gwamnati, jim kadan bayan kammala taron majalisar zartarwa a ranar Laraba.

Sai dai Mohammed, wanda ya ce da safiyar Laraba kamfanin ya aiko da goron gayyatar, bai fadi lokaci da inda za a yi zaman ba.

Hakan na faruwa ne kwanaki, bayan da wasu jami’an diflomasiyya kasashen duniya, suka zauna tare da ministan kula da harkokin wajen Najeriya Geoffrey Onyeama, inda suka nuna rashin jin dadinsu da matakin, wanda suka ce zai take ‘yancin fadin albarkacin baki.

Najeriya ta haramta amfani da shafin a makon da ya gabata, inda ta zargi kamfanin da yin barazana ga zaman lafiya a kasar.

Ta kuma zargi kamfanin da nuna goyon baya ga masu ta da kayar baya a kudu maso gabashin Najeriyar, wadanda Buhari ya ja wa kunne – gargadin da Twitter ya goge, matakin da har ila yau ya fusata hukumomin Najeriyar.

Gwamnatin Najeriya ta zargi dandalin wanda ke da mabiya sama da miliyan 39 a kasar, da ruruta wutar rikice-rikice a sassan kasar.

Kamfanin na Twitter ya haramta wallafa bayanai da ka iya ta da husuma ko nuna kyama ga wani ko wasu, ka’idar da ya ce Buhari ya take.

Kusan mako guda kenan ana ta ka-ce-na-ce a Najeriya dangane da haramcin da hukumomin Najeriya suka saka wa kamfanin, matakin da ke shan suka a ciki da wajen kasar.

Hukumomin Najeriya sun ce matakin ya yi tasiri, yayin da wasu ke nuna akasin hakan, lura da cewa wasu na iya amfani da kafar VPN wajen shiga shafin.