Shugaba Recep Tayyip Erdogan na kasar Turkiyya, yayi tayin shiga tsakani domin tattauna mafita daga fadan da ake a tsakanin rundunar gwamnatin Habasha da ‘yan Kungiyar TPLF na yankin Tigray. 

Erdoghan ya ce, yana da mahinmanci a dauki matakin shawo kan rikicin, domin ceto kasar daga durkushewa, ya kara da cewa, rikicin zai iya yin munmunan illa ga sauran kasashen yankin idan aka ci gaba da zura ido ba tare da an dauki wani mataki dakatar da fadan ba.

Ya dai fadi hakan ne a yayin wata ganawa da manema labarai da yayi da Firaiministan Abiy Ahmed da yanzu haka ke ziyarar aiki a kasar ta Turkiyya. Babu dai karin bayani kan cimma wata matsaya kan batun tattauna mafitan da shugaba Erdogan yayi magana a kai. 

Tun dai a watan Nuwambar bara, fada ya barke a Habasha, dubban dubata sun tsere daga kasar a yayin da wasu sama da dubu dari hudu, ke fuskantar barazanar matsananciyar yunwa inji Majalisar Dinkin Duniya.