Tunisiya ta garkame dan majalisa | Labarai | DWA ranar Lahadin da ta gabata ce dai shugaban na Tunisiya ya kori firaminista sannan ya dakatar da ayyukan majalisar kasar na wata guda, ya kuma bai wa kansa cikakken iko.

Matar dan majalisar da aka kama din ta ce kusan mutane 20 ne suka kutsa kai cikin gidansu inda suka gabatar da kansu a matsayin jami’an tsaro daga fadar shugaban kasa. Matar ta kuma yi zargin cewa sun yi amfani da karfin tuwo a kan mijin nata kafin su yi awon gaba da dan majalisar mai sukar shugaban kasa.

A gefe guda kuma a wannan Jumma’a wata kotu a Tunisiyan ta fara sauraron shari’ar wasu mutane hudu ‘yan jam’iyya Ennahda ta Musulmi masu adawa da shugaban kasar, ana kuma zargin su da tayar da hankula bayan rusa gwamnatin da Shugaba Saied ya yi.
Leave your vote

You may also like

Log In

Forgot password?

Forgot password?

Enter your account data and we will send you a link to reset your password.

Your password reset link appears to be invalid or expired.

Log in

Privacy Policy

Add to Collection

No Collections

Here you'll find all collections you've created before.