Rahotanni daga jihar Tarabar Najeriya na cewa tsohuwar ministar mata Hajiya Aisha Jummai Alhassan ta rasu.

Sadiq Ango, da ga marigayiya, ya tabbatarwa da Muryar Amurka rasuwar mahaifiyar tasa.

Tsohuwar ministar wacce ake wa lakabi da “Mama Taraba” ta rasu ne a birnin Alkahira na kasar Masar a cewar Ango.

A shekarar 2015, Alhassan ta yi takarar gwamnan jihar Taraba karkashin tutar jam’iyyar APC mai mulki, amma ta sha kaye a hannun Gwamna mai ci Darius Ishaku na jam’iyyar PDP.

Ta kuma sake yin takarar kujerar a shekarar 2019 karkashin jam’iyyar UDP. amma gabanin hakan, bayan da ta fadi a zaben 2015, Shugaba Muhammadu Buhari ya nada ta mukamin ministar mata.