Tsohon sanata daga Bayelsa ya koma APC


Sanata Nimi Barigha-Amange wanda ya wakilci a mazabar gabashin Bayelsa a majalisar dattawa daga shekarar 2007 – 2011 ya sauya sheka daga jam’iyar PDP zuwa APC.

Barigha-Amanghe wanda na daya daga cikin wadanda suka kafa jam’iyar PDP ya mika takardar da ta samu sahalewar shugaban jam’iyar APC na Mazaba II dake karamar hukumar Nembe ga hannun sakataren rikon jam’iyar na kasa, Victor Giadom a sakatariyar jam’iyar ta kasa.

Ya alakanta ficewar sa daga jam’iyar PDP da abin da ya bayyana da halayyar mulkin mulaka’u ta gwamna, Seriake Dickson wanda ya zarga da tsayar da kansiloli 105 da kuma ciyamomi 8 shi ka dai ba tare da tuntubar sauran masu ruwa da tsaki na jam’iyar.

Jam’iyar PDP a jihar Bayelsa na cigaba da fama da rikici tun bayan zaben fitar da gwanin yan takarar gwamna da aka gudanar.

Cikin watan Nuwamba me zuwa ne za a gudanar da zaben gwamna a jihar.

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like