‘Yan uwan marigayi Ibrahim Mantu sun bayyana labarin rasuwarsa sa ne da sanyin safiyar Talata, inda suka ce Allah ya yi masa cikawa ne a tsakar daren Litinin, a wani asibiti da ke babban birnin tarayya Abuja.

A wata sanarwa da ‘yan uwan margarin suka wallafa a kafar sada zumunta ta WhatsApp, sun ce Sanata Mantu ya yi jinya a gida kafin ciwon ya yi tsanani aka garzaya da shi asibiti, inda rai ya yi halinsa.

Marigayi sanata Ibrahim Mantu dan kasuwa ne kuma dan siyasa, babban jigo a jam’iyyar PDP wanda ya yi fice a siyasar Najeriya.

Mantu ya taba rike kujerar mataimakin shugaban majalisar dattawan Najeriya a zamanin gwamnatin tsohon shugaban Najeriya Cif Olusegun Obasanjo daga shekarar 1999 zuwa 2007.

An haifi marigayin Ibrahim Mantu a karamar hukumar Gindiri ta Jihar Filato, kuma rasuwarsa na zuwa ne kwana hudu bayan rasuwar tsohon babban sakataren gwamnatin tarayyar Najeriya kuma shugaban kwamitin karbar mulki ga shugaba Muhammadu Buhari a shekarar 2015, Ahmed Joda.

Allah ya jikansa da rahama