Tsohon babban sufeta janar, Gambo Jimeta ya rasu


Tsohon babban sufetan yan sanda, Alhaji Gambo Jimeta ya rasu.

Jimeta wanda aka sanar da mutuwarsa da maraicen ranar Alhamis, ya kasance babban sufetan yan sandan Najeriya daga shekarar 1986 zuwa 1990 inda Aliyu Atta ya maye gurbinsa.

Ya kuma taba zama mai bada shawara kan harkokin tsaro ga tsohon shugaban mulkin soja, Janar Ibrahim Badamasi Babangida.

Mai magana da yawun shugaban kasa, Mallam Garba Shehu ya tabbatar da mutuwar tsohon sufeta janar din cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Alhamis.

A fadar Shehu shugaban kasa, Muhammad Buhari ya bayyana alhininsa kan mutuwar kana ya mika sakon ta’aziya ga iyalan mamacin.


Like it? Share with your friends!

0

You may also like