Tsigewa: Trump zai dauki fansa | Labarai | DWKazalika ya lashi takobin daukar fansa ga duk wanda ya taimaka wurin tunbuke shi da majalisar kasar ta yi bayan da ya sauka daga mulki.  A ranar Asabar ne dai Trump ya hau munbari a wani gangami na siyasa a Jihar Ohio  a karon farko tun bayan saukarsa daga mulki, inda ya yi jawabi yana mai cewa

”Ba za mu taba hakura ba, ba kuma ba za mu taba komawa gefe guda ba. A siyasarmu babu alamar yin saranda. Ya ku ‘yan uwana Amurkawa, har yanzu akidarmu tana nan ba ta canza ba. Abubuwan da suka wakana a baya somin tabi ne kawai.’‘ 

Trump dai ya samu sukunin yin wannan jawabi ne a gangamin siyasar da aka shirya don neman jam’iyyar Republican ta tsayar da dan takarar majalisar wakilan Amirka daga Jihar Ohia, inda Max Miller tsohon hadimin Trump a Fadar White ke neman kwace takarar jam’iyyar Republican din daga hannun dan majalisa mai ci wato Anthony Gonzalez wanda ke cikin ‘yan majalisu 10 na Republican da suka goyi bayan tsige Shugaba Trump bayan da aka zargi tsohon shugaban na Amirka da ingiza ‘yan daba su kawo rudani a cikin ginin majalisar kasar na Capitol a lokacin da ake hatsaniyar zaben kasar da ya gabata.
Leave your vote

You may also like

Log In

Forgot password?

Forgot password?

Enter your account data and we will send you a link to reset your password.

Your password reset link appears to be invalid or expired.

Log in

Privacy Policy

Add to Collection

No Collections

Here you'll find all collections you've created before.