Tsaro: Za A Kafa Sansanin Sojojin Sama A Yankin Funtua, Jihar Katsina


Gwamnatin jihar Katsina karkashin jagorancin Gwamna Aminu Bello Masari ta baiwa rundunar sojojin sama wani fili dake a wani kauye mai suna Gwauruwa dake karamar hukumar Funtua domin kafa sansanin sojojin sama.

Wannan yunkuri da gwamnati take yi, yana daya daga cikin hanyoyin da take so ta bi domin kawo karshen rashin tsaro a jihar.

Matsalar rashin tsaro ta addabi wasu sassa na jihar ta Katsina, inda ta dalilin hakan wasu sukan yi kaura su bar garuruwan su, saboda rashin zaman lafiya a yankin.

Yankin Funtua yana daya daga cikin yankunan da barayi suka addaba a jihar Katsina, a kokarin gwamnatin na ganin ta kawar da matsalar shine ya sa ta yanke shawarar kafa sansanin sojoji a yankin.

Gwamna Masari ya kaddamar da filin ga rundunar sojojin, inda ya mika shi ga kwamandan JB Wing, wanda ya wakilci shugaban rundunar sojojin na kasa baki daya Sadiq Abubakar.


Like it? Share with your friends!

0

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like