Gamayyar kungiyoyin tsagerun dake yankin Niger Delta sun bukaci a kori Apochi Sulaiman kwamandan rundunar sojoji ta JTF dake yankin kan zarginsa da hannu a satar danyen mai.

Kungiyoyin na zargin kwamandan da hannu a satar danyen mai da ake a yankin.

A wata sanarwa dake dauke da sahannun ƙungiyoyin tsageru 13 dake yankin wacce aka fitar ranar Alhamis, gamayyar kungiyoyin sun ce sun binciki zarge-zargen da ake wa shugaban na JTF kuma sun same shi da aikata laifi.

Kungiyoyin sun ce ayyukan rundunar ta JTF na kawo koma baya ga cigaban tattalin arzikin yankin da kuma kasa baki ɗaya.

Sun kuma shawarci hukumar yaki da yiwa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati, EFFC da ta binciki kwamandan rundunar.

Najeriya dai tana asarar miliyoyin daloli a duk shekarar saboda yadda ake satar danyen mai a yankin na Niger Delta.

A lokuta da dama ana zargin jami’an tsaro da hannu a satar man da ake a yankin zargin da suke musaltawa ako da yaushe.