Toshon babban sifetan ƴansanda, Sulaiman Abba ya tsaya takarar sanata a APC


Toshon babban sifetan ƴansanda na kasa, Sulaiman Abba ya sayi fom din takarar sanata a karkashin jam’iyar APC ranar Litinin a sakatariyar uwar jam’iyar dake Abuja.

Tsohon jami’in tsaron na neman samun tikitin jam’iyar na yi mata takara a mazabar Jigawa ta tsakiya.

Abba ya fadawa manema labarai cewa ya shiga takarar ne domin bayar da gudunmawarsa wajen kawo cigaban ƙasa.

Jam’iyar APC ta ware ranar 27 ga watan Satumba a matsayin ranar zaben fidda gwani na kujerar sanata a jam’iyar.

Ya kara da cewa kishin al’ummar sa da kuma nasan ya bautawa kasa shine dalilin da yasa ya shiga siyasa.

A baya dai gwamnatin shugaban kasa, Gudluck Jonathan ta sauke shi daga kan mukaminsa a cikin watan Afirilun shekarar 2015 bayan da ta zarge shi da taimakawa jam’iyar APC a zaɓen shekarar 2015.

Sai dai a wata tattaunawa da ya yi da jaridar Daily Trust, Abba ya musalta zargin inda ya ce ya yi aikinsa ne a zaben kamar yadda doka ta tanada.


Like it? Share with your friends!

-1
93 shares, -1 points

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like