Tawagar yan kwallon Super Eagle ta isa Russia


Tawagar ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Najeriya, Super Eagle ta isa kasar Russia domin buga gasar cin Kofin Duniya.

Tawagar ta Super Eagle ta bar kasar Ausria inda suka gudanar da atisaye da kuma wasan sada zumunci da kasar jamhuriyyar Czech a shirye-shiryen tunkarar gasar.

Yan kwallon da kuma jami’an dake kula da su na sanye ne cikin tufafi na musamman dinkin gida mai launin fari da kuma ratsin kore.

Shigar ta yan kwallon ta kayatar da mutane da dama kuma hakan yasa suka banbanta da sauran yan kwallon kafa na sauran kasashe 31 da yawancinsu ke sanye da riga kwat da nakatayel.

Wannan ne karo na shida da Najeriya ke halartar gasar cin kofin duniya tun bayan da ta fara halartar gasar a shekarar 1994.

Ƙungiyar ta Super Eagle za ta buga wasanta na farko da kasar Crotia ranar 16 ga watan Yuni.


Like it? Share with your friends!

-2
78 shares, -2 points

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like