Tawagar yakin neman zaben Atiku ta isa birnin Fatakwal


Tawagar yakin neman zaben,Atiku Abubakar dantakarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP ta isa garin Fatakwal babban birnin jihar Rivers.

Birnin na Fatakwal da mutane da dama sukewa lakabi da babban birnin yankin Niger Delta mai arzikin mai ya cika makil da ‘ya’yan jam’iyar PDP dake sanye da kaya iri daban-daban masu launin tutar jam’iyar.

A baya dai magoya bayan jam’iyar APC na hasashen cewa akwai sabani tsakanin gwamnan jihar, Nyesom Wike da kuma Atiku Abubakar sai dai taron na yau zai kawar da duk wani shakku da mutanen suke da shi.

Jihar Rivers na daya daga cikin jihohin Najeriya dake da yawan masu kada kuri’a.

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like