Tawagar gwamnatin tarayya ta duba aikin titin Kano zuwa Abuja


Gani yadda aikin ginin hanyar Kano zuwa Abuja ke cigaba da tafiyar hawainiya yasa gwamnatin tarayya ta aike da wata tawaga ta musamman domin duba halin da ake ciki game da aikin.

Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje shi ne ya tarbi yan tawagar a filin jirgin sama na Mallam Aminu Kano dake Kano.

Tawagar ta kunshi shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa, Farfesa Ibrahim Gambari, ministar kudi,Zainab Shamsuna Ahmad da kuma ministan ayyuka da gidaje, Babatunde Fashola.

Tawagar ta duba yadda aikin yake tafiya tun daga Kano zuwa Kaduna inda acan ne za su gudanar da taron masu ruwa da tsaki kan aikin titin.

Mutane da dama dai sun dade suna kokawa kan yadda aikin yake tafiya duba da tsawon lokacin da aka dauka ba ayi wani aikin azo a gani.


Like it? Share with your friends!

0

Comments 31

You may also like