Tankokin Mai Sun Kama Da Wuta A Hanyar Abuja-KadunaGobarar ta barke a kan hanyar Abuja zuwa Kaduna a wawajen Tafa da ke jihar ta Kaduna.

Motocin tanka ne dauke da mai ne suka kone a garin na Tafa. Dama garin na Tafa ya zama  wurin taruwar manyan motocin  tankokin man fetur, wanda yanzu akan aukuwar wannan gobarar ta sa dole matafiya suka fara bin hanyar Jere zuwa Abuja.

Sai dai har yanzu rahotanni ba su tabbatar da adadin asarar rayukan da aka yi ko konewar gidajen ke kasa da inda gobarar ta auku. 


Like it? Share with your friends!

0

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like