Tambuwal Da Yari  Sun Kashe Naira  Miliyan 100 Wajen Gyaran Hanyar Sokoto Zuwa Gusau  


Gwamnatocin Sokoto da Zamfara sun hada hannu wajen gyaran babbar hanyar gwamnatin tarayya mai tsawon kilomita 204 da ta hada manyan biranen jihohin biyu.

Imam Imam, mai magana da yawun gwamnan jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal, shine ya bayyana haka a wata sanarwa da yafitar yau Litinin inda yace an kashe naira miliyan 100 wajen gayran hanyar.

Yace hanyar wacce ta hada jihohin Sokoto,Zamfara, Kebbi  da kuma Kaduna an gyara tane domin rage wahalhalun da matafiya ke fuskanta a hanyar da kuma  rage faruwar hatsura.

Mai magana da yawun gwamnan yace gwamna Abdulaziz Yari na jihar Zamfara shine ya gyara hanyar daga Gusau zuwa Tureta yayin da gwamna Tambuwal ya gyara daga Tureta zuwa cikin garin Sokoto.

“Jihohin guda biyu sun hada kudade wajen gyaran hanyar saboda itace babbar hanyar da ta hada manyan biranen jihohin biyu, da kuma sauran sassan Najeriya,tana daga cikin hanya mafi muhimmanci a yankin arewa maso yamma, saboda ta hade da hanyoyin da suka dangana zuwa Jamhuriyar Nijar, “sanarwar tace.

“Babban abu mai muhimmanci shine a kawar da dukkanin ramukan da suke hanyar, kuma an samu nasarar cimma wannan buri. Wannan kokarin ya kawo sauki ga ababen  hawa dama fasinjoji masu bin hanyar,   kuma hakan ya kawo saukin fitar da amfanin gona saboda yankin na daga cikin inda akafi noma a kasarnan.”

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like